Bayan Zaben Gwamna 18 ga Watan March…Nigeria Elections Diary: A View from Kano on the Gubernatorial Elections by Mallam Usman Aliyu (in Hausa)

Earlier this month, I posted Mallam Usman Aliyu’s Hausa-language Nigeria elections diary (a work I commissioned for this blog). Below is Mallam Usman’s follow-up, treating the gubernatorial elections held on March 18 in 28 of Nigeria’s 36 states. One major noteworthy result of the gubernatorial election was the decisive victory in Kano by the New Nigeria Peoples Party (NNPP), headed by former Governor Rabiu Kwankwaso. Mallam Usman discusses the dynamics in Kano, noting in particular the collapse of the People’s Democracy Party (PDP) there, and gives a detailed account of how voting unfolded, including citizens’ close scrutiny of the collation process.

BAYAN ZABEN GWAMNA 18 GA WATAN MARCH

A Ranar Asabar 18 ga watan March 2023 aka gabatar da babban zaben Gwamnoni a Jihar Kano dama kasa baki daya.

Alhamdulillah anyi zabe lafiya kamar yadda akayi ta addu’a duk da an samu matsaloli a wasu gurare kadan amma abin farin cikin shine ba’a samu asarar rayuka ba saidai an fasa akwatin zabe a gurare wasu guraren kuma an samu aringizon kuri’a (over voting) wanda hakan yasa aka soke zaben wasu akwatuna yayinda kuma wasu kananun hukumomi za’a sake zabe sakamakon kuri’un da aka soke yawansu ya huce na tazarar da aka samu tsakanin wanda yayi nasara da kuma wanda ya biyo baya.

Tabbas zaben 2023 ya kafa wani tarihi ko ace yazo da wani salo na musamman da ba’a taba ganinsu a zabukan da suka huce ba. Misali fitowar da mutane sukayi wannan zabe musamman mata adadin mutanen da suka kada kuri’a a wannan zabe yafi adadin wanda suka kada kuri’a a zaben shugaban kasa da sanata, duk da anyi barazana sosai da kuma hasashen za’a iya samun tashin-tashina a wannan zabe amma cikin hukuncin Ubangiji da kuma addu’o’i komai yazo da sauki. Salon da wannan zabe yazo dashi shine Jam’iya mai mulki tayi amfani da wasu abubuwa domin bawa masu zabe su zabesu kamar Atampa, Shadda, Taliya, Omo da sauransu abin mamakin shine daga farkon zabe wannan abubuwa da suke rabawa sunyi tasiri matuka domin mutane da yawa sun zabesu saboda dalilin wannan abubuwa da suke bayarwa yayinda wasu kuma suna karba amma sai su zabi wanda sukeso, masu dabara a ciki kuma sai suke amfani da idan kinaso ko kanaso idan layi yazo kanka zasu Hada ka da agent dinsu ka zaba a gabansu sannan idan ka fito su baka wata takarda mai kamar pass sannan su fadamaka inda zakaje ka karbi kayanka.

Daga fara zabe zuwa wajen 11 na rana akwatuna da dama jam’iya mai mulki ce akan gaba ciki harda akwatin da nayi zabe amma daga lokacin da jama’a suka fahimci kayan da ake rabawa fa sun kare sai labari yasha ban-ban sai kowa ya koma yana zabar raayinsa wanda hakan ya bawa jam’iya adawa damar lashe zabe a kaso 80 cikin 100 na akwatunan Birnin Kano da kewaye.

Babban abin mamaki da kuma daukar hankali a wannan zaben shine yadda Alumma bayan sunyi zabe basu tafi gidajensu ba suka tsare kuri’arsu kuma suka raka akwatunansu har Collation Centre, na fara mamaki tun daga lokacin da ake raba Ma’aikatan zabe zuwa guraren da zasuyi aiki domin karfe 3 na dare amma jama’ar gari ne suke tsare da maaikatan zabe wasu a machine wasu a mota wasu ma a kafa. Dan motar da yawancin maaikatan suka hau zuwa voting centres domin kada kuria babu jami’in tsaro a ciki haka mutanen gari suka raka su kuma suka jira aka raba har akwatin da zamuyi zabe yayinda da yawa daga cikin masu zabe a akwatuna suka rike kayan aiki tare da basu abunda zasu karya kafin a fara aiki.

An samu nasara sosai a wannan zaben wajen fara zabe da wuri ba kamar zaben daya gabata ba domin karfe 7:25 yawancin maaikatan suka isa inda akwatunsu yake saida 8:30 tayi sannan suka fara aiki hakan ya bada nasarar gama zabe da wuri a gurare da dama duk da jama’a sun fito da yawa fiye da zaben daya gabata amma wasu guraren karfe 12, wasu 1 sun kammala zabensu, hukumar shirya zabe ta INEC tayi kokari matuka wajen fara komai akan lokaci kuma ta tsara komai na aikin zabe, sannan matsalolin da aka samu da na’urar tantancewa (BVAS) a zaben daya gabata ko kadan ba’a sameta a wannan zaben ba, sannan korafin da agents sukayi a zaben daya gabata na rashin dora sakamakon zabe a website na INEC wannan zaben kowane akwati saida aka dora zaben immediately bayan kammalawa hakan yasa mutane suka fara ganin sakamakon zabe tun kafin tafiya tayi nisa, wannan dalilai sukasa mutane da dama kama daga ma’aikatan zabe zuwa alummar gari suke ganin ba’a taba yin sahihin zabe a Nigeria kamar wannan zabe na Ranar 18 ga Watan March, an samu tsaro sosai wanda haka yayi maganin masu yunkurin tada hankali a guraren zabe.

Kananun jam’iyu sun bada mamaki ciki harda jam’iyar data lashe wannan zabe ta NNPP kasancewar sabuwar jam’iya ce da batafi watanni 8 ba amma tayi nasarar lashe zabe a jahar da ake ganin itace kan gaba wajen yawan alumma a Arewaci dama kasa baki daya, hakan yasa siyasar wannan lokaci ta dauki wani yanayi da kuma salo na musamman da ba’a saba ganinsa a zaben da suka huce ba. Tarihi ya nuna Margayi Abubakar Rimi ne kadai ya taba daukko sabuwar jam’iyar da bata dade kuma ba’a santa ba tayi nasara a Jihar Kano sai wannan karon da Rabiu Musa Kwankwaso ma ya kafa wannan tarihin.

Sannan ba’a taba zaben da hankalin Jama’a gaba daya yana kansa ba kamar wannan zaben mutane da dama sun bada gudummawa ta fanni daban daban ciki harda wanda basuda wata alaka da yan takarar da suka shiga wannan zabe, nasan mutane da dama wanda sukayi amfani da abun hawansu wajen daukar mutane su kaisu guraren da zasuyi zabe musamman wanda aka canjawa akwati aka kaisu wani waje mai nisa, sannan da yawa mutane maza da mata basuyi cikakken bacci ba tun daga ranar da akayi zabe zuwa ranar da aka sanar kowa ka gani kansa yana kan waya yana dubawa ko kuma kunnensa yana radio yana saurarar sakamakon zabe, Tabbas soyayyar da jama’ar gari suka nunawa Jam’iyar data lashe a yanzu ba karamar soyayya bace.

A ranar Litinin 20 ga watan March aka sanar da sakamakon zabe na Jihar Kano inda sakamakon manyan yan takara guda 5 ya fito:1. Abba Kabir Yusuf NNPP ya samu kuri’a 1,019,6022. Nasir Yusuf Gawuna APC ya samu kuri’a 809,7053. Sadiq Aminu Wali PDP ya samu kuri’a 159,574. Mal Ibrahim Khalil ADC ya samu kuri’a 12,8325. Sha’aban Ibrahim Sharada ADP ya samu kuri’a 9,402. Abin mamaki a wannan zabe shine yadda Jam’iyar PDP ta kasa kai bantanta duk da kasancewarta babba jam’iya a kasa baki daya amma a duka zabukan da aka gudanar. Jam’iya PDP bata samu koda Dan Majalissar Jaha guda daya ba sai ma kokarin da sabuwar Jam’iyar ADC (Mal Ibrahim Khalil) yayi wajen kamo jam’iyar PDP a wannan zabe, a fili ya nuna Jam’iyar PDP batada wani tagomashi a jahar Kano kuma tabbas suna bukatar daukar matakai matukar suna bukatar farfado da martabar jam’iyarsu. Daga ranar da aka sanar da wannan sakamako har zuwa jiya Laraba Alummar gari murna suke suna celebration yayinda wasu suka fara tattaki daga inda suke zuwa Kano a kafa domin nuna soyayyarsu ga wanda ya lashe wannan zabe saidai an jiyo shi wanda ya lashe wannan zabe yana garesu da suyi hakuri su koma gida sakamakon rashin tsaro da kuma sace-sacen mutane da ake fama dashi bugu da kari kuma ga shigowar azumi ya bukaci duk masoyinsa da yayi masa adduar nasara wajen gudanar da mulkinsa. A washe garin ranar da aka fadi Sakamako ranar Talata kenan Jam’iya mai mulki ta hada wani taron manema labarai domin sanar da jama’a matsayarsu akan wannan zabe inda mai girma mataimakin Gwamna kuma dan Takarar Gwamna ya tabbatar da cewa basu yarda da wannan zaben ba har yayi ikirarin yakamata yayi ace wannan zabe ya zama Inconclusive tare da tabbatar da zasuyi zanga zanga a ranar Laraba kuma zasu shiga kotu domin neman hakkinsu, saidai fa jama’a sonata tofa albarkacin bakinsu akan wannan Magana inda mutane suke cewa ashe kiran Kaddarar da yakeyi a lokacin neman zabensa ba gaskiya bane domin kuwa ya fadi wasu kalmomi guda 2 wanda ya kasa cika koda 1 daga ciki, 1. Yace idan mulkin Kano ba alkhairi bane a gareshi Allah karya bashir gashi Allah bai bashi ba amma gashi kamar bai yarda ba. 2. Ya fada a gaban jama’a a taron BBC cewar duk wanda Allah ya bawa wannan kujera zasu mara masa baya kuma su bashi shawarwari na gari ba tare da cin dunduniya ba amma shima gashi ya gaza cika maganarsa. A jiya laraba dai suka gabatar da Zanga Zangar neman hakkinsu ga hukumar INEC yayinda hakan ya zama abin dariya a garesu.Wannan zabe ya kafa wasu tarihi guda biyu a wannan shekara1. A duk jahohin Nigeria babu dan Takarar Gwamnan daya samu Kuri’a Million Daya sai a Kano kuma a karkashin sabuwar Jam’iyar NNPP.2. A tarihin Nigeria gaba daya wannan ne karo na farko da tsagin gwamnati sukayi zanga zanga akan neman hakkinsu.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s