Editor’s Introduction (by Alex Thurston):
Nigeria held presidential and legislative elections on February 25, and will hold state elections on March 18. I asked an old friend and colleague, Mallam Usman Aliyu of Kano, if he would be willing to keep an election season diary and allow me to publish it here. For over a decade, Mallam Usman’s observations about local and national politics have shaped and informed my own understanding of Nigeria. Although written in the moment, I think these entries already have staying power. Below is the Hausa text. I will briefly summarize here:
In the first entry (from February 10), Mallam Usman reflects back on the party primaries and what he sees as a vigorous, four-way competition for the presidency between Bola Tinubu, Atiku Abubakar, Peter Obi, and Rabiu Kwankwaso. He also discusses the allegations of ill-health and corruption that Tinubu and Atiku’s campaigns leveled at one another, and also covers in detail the gubernatorial candidates in Kano (the most populous state in the north).
In the second entry (from February 21), Mallam Usman describes the mood in Nigeria and in Kano on the eve of the elections, especially amid the cash shortages – and he brings in ordinary people’s views of why outgoing President Muhammadu Buhari authorized the controversial effort to exchange old bank notes for new ones.
In the third entry (from March 1), Mallam Usman analyzes the election results and describes people’s reactions to them and to the conduct and the expense of the elections. He concludes by noting that some in Atiku’s camp felt that Kwankwaso (who won heavily in Kano) in some way tipped the election to Tinubu.
In any case, these brief summaries don’t do the full diary justice. Hausa speakers may be interested to read the whole thing.
February 10, 2023
ZABEN 2023
Duba da lokacin da muke ciki a yanzu, zabe ya gabato, wato zaben Shugaban Kasa da na sauran mukamai: Gwamnonin jihohi da kuma na yan majalisun tarayya da na jihohi wanda ake sa ran fara gabatarwa ranar 25 ga wannan watan. Kamar dai yadda hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC karkashin shugaban wato Professor Mahmoud Yakubu ta tsara. Ana sa ran gudanar da zaben Shugaban Kasa da na Yan majalisun tarayya ranar 25 ga watan wanda daga bayan sa zasu gudanar da na jihohin Kasar gaba daya.
Idan mukayi laakari da Manyan Jam’iyunyake da za’a buga zaben sun hada da PDP, APC, NNPP da kuma LP.
APC – ASIWAJU BOLA AHMAD TINUBU
PDP – ALHAJI ATIKU ABUBAKAR
NNPP – ENGR. RABIU MUSA KWANKWASO
LP – PETER OBI
Kowane dan kasa a yanzu yana hasashe ne akan daya daga cikin wannan Jami’iyu shine zai lashe wannan gagarumin zabe, yayinda Mutane da dama sukace wannan zaben fah ya banbanta da sauran zabukan da akayi a baya domin kuwa a cikin yan Takarar da suke cikin wannan Jam’iyu guda 4 ana ganin kowa zai iya lashe wannan da kuma tsarin da Hukumar Zabe INEC wanda ganin baayi Magudin zabe ba kuma baa samu abinda a zaben baya aka samu ba wato (Inconclusive) wanda hakika a zaben 2019 ya zama babban abinda yaciwa Talakawa tuwo a kwarya har suke ganin anyi abinda akayi a wannan zaben, to Alhamdulillah shi Shugaban Hukumar Zabe INEC (Mahmuod Yakubu) ya bada tabbacin cewa a wannan zabe fa babu maganar Magudin Zabe da kuma Inconclusive, sakamakon hakane mutane suke hasashen tabbas wannan zaben fah zai bada mamaki ganin kowane Dan Takara yanada nasa Jama’ar kuma kowane Dan Takara a cikin Mutane 4 din dana lissafa ka iya darewa shugabancin wannan kasa duba ga wasu alkaluma na siyasa da kuma alamu da suke bayyana.
Idan muka faro tun daga Farko wato Zaben Fidda Gwani (Primary Election) manyan jam’iyu irinsu APC da PDP sun sha gwagwarmaya matuka kafin su Fidda guda 1 a ciki ya zama Amintaccen Dan Takara, idan mukayi duba ga APC wato Jam’iya mai mulki an shiga zaben fidda Gwani da yan Takara 10 wanda 3 daga ciki sukafi Shahara sune, Bola Ahmad Tinubu, Yemi Osibanjo da kuma Rotimi Amaechi yayin da Yan Takara 6 suka Janyewa Tinubu daya kuma ya janyewa Osibanjo. Daga karshe dae Bola Tinubu ya lashe zabe da mafificin rinjaye. Sai Jami’iyar PDP inda mutane 3 din da sukafi Shahara sune Alh. Atiku Abubakar, Nyesome Wike da kuma Bukola Saraki. A daya bangaren wato NNPP da kuma LP (Labour Party) basu sha wahala wajen fitar da yan Takararsu ba tun bayan da Engr. Rabiu Musa Kwankwaso ya fice daga Jami’iyar PDP ya shiga Jam’iyar NNPP tare da nuna kudiransa na tsaya musu Takarar Shugabancin kasa haka yasa basu bata lokaci wajen tunani ko kokarin gabatar da Zaben Fidda gwani ba suka bashi wannan Takara domin kasancewarsa sananne kuma goge a harkar siyasa. Sai kuma Peter Obi na Jam’iyar Labour Party shima tun bayan daya Fice daga Jam’iyar PDP ya nuna kudirinsa wajen zamar musu dan Takara basuyi wata-wata ba suka amince domin yayi musu wannan Takarar kasancewarsa masani ne a Siyasa kuma yayi Gwamna a Jihar Anambra.
Akwai labarai da sukayi ta yawo a Kafafen sada zumunta akan Cecekucen dake tsakanin Manyan yan takarar Shugabancin kasar nan wato Atiku Abubakar na Jam’iyar PDP da kuma Bola Tinubu na jam’iyar APC inda Yan takarar suke jefa wa junansu zarge-zarge game da lafiyarsu da kuma cin hanci da rashawa yayin da a lokacin ya rage saura baifi kwana 40 a gudanar da babban zaɓen ƙasar na 2023.
Tawagar yaƙin neman zaɓen Bola Tinubu na jam’iyyar APC mai mulki ce ta fara sukar Atiku Abubakar, na babbar jam’iyyar adawa ta PDP, tana mai cewa ba shi da lafiyar jagorantar Najeriya. Tinubu ya ce ya kamata ‘yan Najeriya su ji da lafiyar Atiku domin shi yana da cikakkiyar lafiyar gudanar da mulki a yayin da suke mayar da martani, tawagar kamfen ɗin Atiku ta zargi Tinubu da aikata cin hanci da rashawa, tana mai ikirarin cewa “Tinubu kansa shi ne cin hanci”. An daɗe ana tafka muhawara kan ƙoshin lafiyar ‘yan takarar shugabancin ƙasa a Najeriya, inda al-uma suke gudun maimaita abinda ya faru a baya bayan da Shugaba Buhari da ke mulki a yanzu ya shafe watanni yana jinya a Birtaniya a wa’adin mulkinsa na farko.
Cikin wata sanarwa da tawagar yaƙin nema zaɓen Bola Tinubu na APC ta fitar sun zargi Atiku Abubakar na PDP da ɓoye ainahin ƙoshin lafiyarsa da kuma cin hanci.
“Lokaci ya yi da Atiku Abubakar zai faɗi gaskiya game da abu biyu: ƙoshin lafiyarsa da kuma yadda ya haɗa baki da tsohon mai gidansa Olusegun Obasanjo wajen sace dukiyar Najeriya,” a cewar sanarwar da mai magana da yawun tawagar ya fitar, Bayo Onanuga.
Mista Onanuga ya ce tawagar Kamfe ɗin Atiku na ɓoye batun lafiyar ɗan takararsu ta hanyar ƙirƙirar ƙarairayi kan nasu ɗan takarar.
“Atiku ne ɗan takarar da ‘yan Najeriya ya kamata su damu a kansa. Ƙarairayi na tsawon lokaci da sauran hanyoyin kawar da hankali sun daina aiki yanzu.
“Tabbas Atiku ba shi da lafiya kuma hanyoyin da ake bi wajen ɓoyewa sun yi kaɗan.”
Da ya ke mayar da martani game da zarge-zargen, kakakin tawagar kamfe ɗin Atiku Kola Ologbondiyan, ya ce abin dariya ne ganin yadda APC ke yi wa ɗan takararsu ƙagen rashin lafiya.
“Kazalika, shashanci ne yunƙurin da Tinubu ya ke yi, wanda ya yi shuhura da zama cin hanci shi kansa, na ɓata sunan ɗan takarar PDP,” in ji shi.
Sanarwar ba ta gushe ba sai da ta zargi Tinubu da mu’amala da miyagun ƙwayoyi. A siyasar Najeriya, ba sabon abu ba ne ‘yan takara su dinga jifan junansu da manyan zarge-zarge irin waɗannan a bainar jama’a. Sai dai kuma ba za a taɓa ganinsu tare suna ce-ce-ku-ce a juna ba ballantana rikici.
Rashin manufofi ne ke jawo irin waɗannan munanan zarge-zarge tsakanin PDP da APC a Najeriya, a cewar Farfesa Kamilu Sani Fagge, wani masanin kimiyyar siyasa a Jami’ar Bayero ta Kano a lokutta daban daban da ya ke yin fashin bakin siyasar Kasar nan.
“Wannan al’amari ya nuna irin yadda siyasarmu take, saboda ‘yan takarar ba su da wani tsari na tunkarar matsalolin da suka addabi ƙasa shi ya sa ake ta zargin juna da kalaman ɓatanci da siyasar banga,” in ji shi.
Farfesa Fagge ya ce irin waɗannan kalamai ba za su yi wani tasiri ba a kan masu zaɓe.
“Ba zai sauya ra’ayin wani mai jefa ƙuri’a ba don ya zaɓi wani takara.”
Haka nan, masanin kimiyyar siyasar na ganin cewa kalaman za su ƙara zafafa yayin da zaɓe ke ƙara ƙaratowa, “amma da zarar an yi zaɓe sai ka ji shuru, a bar magoya baya da cecekuce”.
Wasu daga cikin mutanen Najeriya suna ganin babu babban abinda yake damun Kasar nan a yanzu face cin hanci da rashawa da kuma rashin samun lafiyayyen Shugaban da zai jagorance su kuma suke gudun kara fadawa wannan tarkon. Hakan yayi tasiri sosai wajen sakawa wasu yan Najeriya shakku akan wadannan yan Takara guda 2 wato Atiku da Tinubu, yayinda a daya bangaren kuma Engr. Kwankwaso da kuma Peter Obi suka sake samun damar cigaba da Kamfen da wannan dama da suka samu akan abokan Karawarsu.
A yanzu ya rage baifi saura kwana 10 a shiga babban zabe yayin da yan takara suke ta kokarin zagaya Garuruwa domin jaddada kudirinsu na shugabantar wannan kasa, abunda yake yawo a yanzu shine ikirarin da Dan Takarar jami’iyar APC Bola Tinubu akan an canja kudi kuma ana wahalar mai saboda talakawa su tsani Jam’iyar APC kuma ya fadi zabe a fadarsa kamar kamshin mutuwa yan Jam’iyarsa sukeyi masa, kwatsam sai akaji Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufa’I yana cewa wasu manya a Villa basa goyon bayan Tinubu a yayinda jama’ar Gari kuma suke ganin karara wannan Magana da Mai Girma Buhari yake.
Idan akazo fanin raayi da kuma cancanta mutane da dama sun fadi albarkacinsu da kuma hasashe akan wanda ake tunanin zai iya lashe wannan zabe. Mutane da dama sun fadi raayinsu game da wanda suka cancanta da wanda kuma suke hasashen wanda zai lashe zabe. Wasu sunce indae maganar cancanta ake to fa Bola Tinubi baya cikin wanda suka cancanta sakamakon shekarunsa sunja kuma bashida cikakkiyar lafiya Bugu da kari kuma ana zarginsa da safarar miyagun kwayoyi, bugu da kari kuma ga yanayin da jama’a suke tunanin jam’iyar APC ta saka mutane tun daga lokacin da suka karbi mulkin kasa shekara 8 kenan ga kuma wahalar mai da kudi da ake fuskanta a yanzu da zabe ya gabato, tabbas wannan ka iya shafar shi dan takarar APC Tinubu. Sannan kuma mutanen Arewa suna ganin a cikin manufofin Tinubi babu wani abu da zai amfani yan Arewa, hakan ma yana iya kawo masa nakasu wajen cin zabe.
A daya bangaren kuma mutane da yawa suna ganin Atiku Abubakar ma bai cancanci zama Shugaban kasa ba sakamakon tun daga primary election duk wani abu daya shafi yakin neman zabensa yana amfani da kudi shiyasa ma mutane suke hasashen tabbas idan yaci zabe jama’a zasu sha wahala saboda tunaninsa dan kudinsa aka zabeshi kuma yanada kudirin mayar abubuwa da dama hannun yan kasuwa wanda jama’a suke ganin hakan wahala zai karawa yan Najeriya. Wasu da yawa sunce bashida gogewa da jajircewar da ake bukata saboda mukamin mataimakin shugaban kasa ya rike wanda yake daidai da dan zaman banza kuma baisan kukan talakawa da kuma abinda suke bukata ba. Bugu da kari ga matsalar rashin cikakkiyar lafiya da kuma shekaru da shima suka cimmasa wanda yan Najeriya suna ganin hakan bazai bashi cikakkiyar dammar gudanar da mulkin wannan kasa.
A bangaren Rabiu Musa Kwankwaso kuwa kasancewa ta dan Kano banci karo da rashin cancantarsa da yawa ba saidai masu ganin idan yaci mulki yanada riko kuma baya yafiya shiyasa wasu suke ganin zaiyi amfani da wannan damar wajen Taka duk wanda yakeso wanda kuma talakawan Najeriya bashi suke bukata a yanzu ba. Sannan kuma mutanen kudancin Najeriya suna zargin idan yaci mulki to fa zai karkato da abubuwa da dama zuwa Arewa saboda kasancewarsa mutum mai kabilanci. Wasu kuma suna ganin abinda zai hanashi cin zabe bai huce fitowarsa a cikin karamar jam’iyar da baa dade da kafata ba kuma jama’ar mu musamman na kauyuka sunfi sanin jam’iyar PDP da APC kuma wannan babban nakasu ne ga Rabiu Kwankwaso.
A qarshe idan mukazo maganar Dan Takarar Labour Party wato Peter Obi kaso 95% na mutanen arewacin Najeriya basu san Peter Obi ba saboda dalilai guda 2 na 1, Ya fito a Jam’iyar da baa santa ba na 2, baiyiwa Najeriya wani abun azo a gani da har zasu sanshi ba. Da yawa suna ganin idan ma ace an sanshi kamar sauran Yan Takara to fa bashida gogewar mulki kasancewar Gwamna yayi a wani karamin garin da baifi yawan mutanen Local Government daya ba a Kano wato Anambra kuma bashida cikakkiyar nagartar zama Shugaban wannan kasa.
Idan muka dawo batun wanda ake ganin zai iya lashe zabe da kuma dalilai;
1. Dan takarar Jam’iyar APC wato Tinubu zai iya lashe zabe sakamakon da yawa mutanen Lagos suna sonsa kuma ana ganin suna cikin garurwan da suke da yawan al-umma a Najeriya da kuma wanda suke yarensa zasuyi masa kara, sannan kuma idan aka duba wanda ya dauka a Mataimaki Kashim Shatima shima mutum ne mai Jama’a a jahar Borno wanda ka iya taimakawa wajen ganin Tinubu yaci zabe.
2. Dan takarar Jam’iyar PDP Atiku Abubakar kusan shi mutane suke ganin tabbas wannan shekarar tasa ce saboda a zaben baya kusan yayi kankankan da Shugaba Buhari wanda shine akan mulki a wannan lokaci shiyasa suke ganin wannan karon zai iya cin zabe kuma da yawa suna ganin shine zai ceto kasar nan daga halin da take ciki. Sannan mutanen Arewa maso Gabas sunyi alwashin sun gaji da yan Arewa ta ta yamma suna mulkarsu suna shan wahala shiyasa sukace suma fa wannan karon nasu zasu zaba.
3. Dan takarar Jam’iyar NNPC Rabiu kwankwaso shine na 2 a jerin wanda suka kasance favourite saboda masu ganin duk cikin yan takarar yafisu cancanta da kuma gogewar mulki saboda ya riqe mukamai da dama fiye da sauran yan takara hakama yafi dukkan sauran yan takara mataki a karatu wanda da yawa suke ganin matakin iliminsa ya kai ya jagoranci wannan kasa kuma ya ceto ta daga halin da take ciki saboda jajircewarsa a wajen shugabanci kuma ya kasance mai fada da cika duk abinda yayi alkawari a lokacin dayayi mulki a Kano da kuma sauran mukaman daya rike. Mutane da yawa harda yan kudu suna kara bashi nasara saboda mataimakinsa mutum ne mai mutane hakan na iya sawa wasu daga cikin mutanen kudi su zabi kwankwaso saboda mataimakinsa. Duk wanda zai bude baki akansa saidai yafadi wani abun daban amma indae maganar cancanta ake to ba shakka Kwankwaso yafi duk sauran yan takara cancanta.
4. Dan takarar Jam’iyar Labour Party Peter Obi shine na karshe a hasashen mutane sakamakon rashin saninsa da baayi a arewa ba da kuma kasancewa mutanen Arewa sunfi mutanen Kudu yawa hakan zaiyi matukar shafar nasararsa.
BABBAN ZABEN GWAMNA JIHAR KANO
Kimanin kwanaki 25 ko kasa da haka suka rage zaben Gwamna a Jihar Kano, zaben da zai kasance mafi daukar hankali a Arewacin Nigeria. Zabe ne tsakanin Manyan Jami’iyu guda 4;
- Abba Kabir Yusuf (NNPP Party)
- Nasir Yusuf Gawuna (APC)
- Muhammad Abacha (PDP)
- Sha’aban Ibrahim Sharada (ADP)
Idan muka dauki wadannan yan takara daya bayan daya muka tattauna cancantar su da kuma abinda ka iya hana kowannensu hawa wannan kujera zamuyi gamo da abubuwan ban mamaki a ciki;
1. Abba Kabir Yusuf (NNPP) mafi yawan Al-ummar Jihar Kano musamman na cikin Kano da kewaye sun raja’a akan Abba saboda kasancewarsa tare da Rabiu Kwankwaso da kuma duba da nasarar daya samu a zaben daya gabata wanda shine yakasance shiga Zaben sa na farko a siyasa mutane mafi rinjaye suke ganin shine ya dace ya hau wannan kujera musamman yan cikin garin Kano suna ganin wannan lokacin fa dan cikin kwaryar Kano sukeso. Babbar matsalar da zai iya samu bai huce kasancewarsa a sabuwar Jam’iyar da yawanci mutanen kauye basa banbancewa sun fi sanin PDP da APC.
2. Nasir Yusuf Gawuna (APC) ya zama kamar shine na 2 da mutane suke tunanin da hasashen zai hau kujerar mulki wanda dama shine mataimakin gwamna a yanzu. Saidai Jama’a da dama suna ganin rashin cancantarsa saboda abinda suka aikata a zaben daya gabata dashi da Mataimakinsa a yanzu wanda ake ganin rashin sanin darajar Dan Adam ne mutane subi layi cikin rana suyi zabe saboda son zuciya da kwadayin mulki su yaga sakamakon zabe. Wannan ka iya zama babban tabo a gareshi, yayinda wasu da dama suke ganin mutum ne mai fuska 2 yana nuna son hadin kai da kuma taimakawa al-ummar jihar Kano bayan a zuciya da ayyukansa mutane basuga hakan a zahiri ba, sannan kuma ana ganin abubuwan da yake cewa zaiyi idan yah au mulki meyasa a matsayinsa na mataimakin gwamna bai bawa gwamna shawara yayi ba lokacin da yake kan mulki hakan ya fito da yaudara a cikin lamarinsa.
3. Sha’aban Ibrahim Sharada (ADP) fitowar Sha’aban takarar Gwamna ya zama abu mai matukar mamaki a idon mutanen Kano yayinda mafi akasari ma suke zargin takararsa bata gaske bace contract aka bashi wanda daga karshe zai janye ya hada kai da wani. Babban abinda mutane basu fahimta ba shine Sha’aban mutum ne mai al-umma a jihar Kano wanda ko baici zabe ba to fa zai ragewa yan takara kuri’a. Kuma kasancewarsa a cikin karamar Jam’iyar da a cikin gari ma baa santa ba sosai bare kuma cikin kauyuka ka iya bashi matsala a wannan zabe da zaayi.
4. Muhammad Abacha (PDP) Al-ummar Jihar Kano sun gaza gane me yake faruwa a Jam’iya PDP a Kano, yau ace Abacha ne dan takara gobe ace Sadiq Wali shiyasa ma mutane da yawa suke ganin jam’iyar PDP bata shirya shiga wannan zabe da zai gabata nanda kwanakin da basufi 32 ba. Jama’a da yawa suna ganin wannan kamar wasan kwaikwayo ne kuma hakan yasa baa saka jam’iyar PDP a lissafin zaben gwamnan jihar Kano. Idan ma ace Abacha ko Sadiq ne dan takara to fa dukkansu babu abinda suka sani akan siyasa da kuma mu’amala da mutane. Rashin kamfen da basuyi ba sakamakon rigimar cikin gida da suke fama da ita yasa ake ganin to fa tabbas lokaci ya kure musu.
A karshe zan rufe wannan rubutu nawa da cewa tabbas a Kano za’ayi zaben da aka dade baayi kamar sa ba kuma hasashen mutane da yawa ya nuna koma waye zaici wannan zabe to fa zaici ne da fifikon kuri’a kadan saboda yan takarar da suka fito wannan zabe.
A karshe muna Addu’ar Allah ya zaba mana shugabanni na gari wanda suke da niyyar gyara ba wanda Zasu yi wadaka da dukiyar al’umma ba.
Duk da cewa mutane da dama suna ganin wannan zabe ba lalle ne ya yiwu ba amma dai shi shugaban hukumar zaben mai zaman kanta wato INEC Professor Mahmoud Yakubu ya kuma ya sake kuma maimaitawa a kowanne lokaci cewa hukumar sa zata bada mamaki kuma zata gudanar da zabe mafi sahihanci a cikin tarihin zabukan wannan kasa tamu Nigeria.
Wani sabon batu kuma wanda ya fito ranar Talata 7/2/2023 shine wata sanarwa da gamayyar wasu jam’iyu guda goma sha uku a cikin sha takwas suka fidda shine sun cimma matsaya akan cewa akwai yiwuwar ba zasu shiga cikin wannan zabe mai zuwa ba duba da yanayin da alumma ke ciki na halin matsi kama daga wahalar man fetur da kuma matsi dangane da wannan canjin kudi da aka yi duba da dan takaitattecn lokacin da Babban Bankin kasar nan ta bayar wanda ya haifar da matsi da kuma cecekuce a tsakanin mutane, Yan takarkaru da kuma shugannin siyasun kasar nan.idan har hakan ta tabbata to lalle sai mu ce wannan zabe mai zuwa yana fuskantar tazgado wanda kuma ka iya sakawa a daga ko kuma ma zaben ya zamanto ba mai iya yiwuwa ba gaba daya.A halin da ake ciki kuma a yau din nan Laraba 9 ga wata ana ci gaba da samun labarin zanga zanga a garuruwa da dama Kamar Jihar Ogun, Edo, Kogi da sauransu haka kuma a na ci gaba da samun labarin mutane a jihohi daban daban suna lalata na’urar ATM da kuma yunkurin farmaki ga bankuna duka dai domin nuna rashin jin dadi kan wannan batu. wannan dai shine halin da Kasar nan ta samu kanta wanda kuma ka iya jawowa a dage zaben ko kuma ma hana iya gudanar da zaben ma gaba daya.
February 21, 2023
Yayin da ya rage saura kwana 3 daidai a shiga babban zaben shugaban kasa da yan majalissar tarayya kuma ake gab da rufe yakin neman zabe (campaign), Jama’a na kara kokawa kan matsin rayuwa da ake ciki sakamakon canjin kudin da aka samu yayinda hakan ya bude fuskoki guda 2 a bangaren siyasa.
Na 1 wasu daga cikin gwamnonin Arewa da suka kasance yan jam’iya mai ci a yanzu wayo APC suna ganin kamar shugaban kasa fa kamshin mutuwa yakeyi musu saboda yana ganin shi fa ya gama mulkinsa shiyasa bai damu su ci zabe ko su fadi ba kuma hakan ya nuna kamar akwai wata a kasa tsakanin su da gwamnonin da kuma shi shugaban kasa.
Amma a cewar shugaba Buhari an yi wannan canjin kudi ne sakamakon yaji kishin-kishin cewar manyan yan siyasa musamman Gwannoni sun tanadi kudade masu tarin yawa domin suyi amfani dasu lokaci zabe domin siyan kuri’ar talakawa, wanda shugaban yake ganin hakan ya saba da dokar kasa, kuma yunkurin da yakeyi a yanzu zaa iya cewa yana iya kokarinsa wajen ganin a wannan zabe na 2023 an gabatar da zabe sahihi kuma mai inganci.
Na 2 a bangaren talakawan gari kuma suna kokawa matuka sakamakon wahalar kudi wanda suke ganin ya zama kamar rijiya ta bayar da ruwa guga ya hana, mutane sun yi aiki tukuru wajen neman kudi amma kashe su ya zama wahala, duk inda ake samun kudi (cash) sun zama samunsu wahala koda zaka samu kuwa sai kabi dogon layi kuma ranka ya baci sannan a karshe ma bazaka samu abinda zai isheka ba. Ya zama abinda ake cewa kaida kudinka amma saidai idan zaka fita kaje wajen masu POS kamar kana maular su taimaka maka da abinda zakayi transport kuma kaci abinci, Jama’a da dama sun ce wannan wahala da ake basu DANBAKARA suda jam’iya mai mulki yayinda kowa yake Allah wadai da wannan matsin rayuwa.
Wasu tunanin su shine Shugaban kasa yayi wannan canjin domin tabbatar da sahihin zabe saidai ya zama abinda hausawa suke cewa bayan wuya sai dadi to tabbas wannan itace wuyar kuma idan muka jure da yardar Allah a cewar su zamu samu dammar zabar shugabanni da kanmu kuma zaa bamu wanda muka zaba.
Zaben bana yazo da tsaruka na musamman ba kamar wanda akayi a baya ba domin na samu tattaunawa da waddanda suke zuwa yin training na aikin zaben wanda aka fara ranar Juma’a, kamar yadda suka Gani dai gaskiya ne zaben ya zo da sababbin abubuwa kamar amfani da na’urar BVAS wajen tantance duk wanda zai kada kuri’a kuma a wannan zabe babu zancen tantance mai yin zabe ta hanyar takarda wato (manual identification) sai na’urar BVAS ta tantanceka sannan zaka samu dammar kada kuri’a.
A Daya bangaren kuma abinda mutane suke fada na cewa anya zaayi zaben nan ba tare da an daga ba na iya faruwa saboda alamu sun nuna karara hukumar gudanar da zabe INEC batada isassun kudaden gabatar da wannan zabe, akwai littafin da ake amfani dashi wajen bawa masu aikin zabe wato (Manual) a zaben baya an bawa kowane ma’aikaci nasa amma wannan zaben sai gashi an buge da hada ma’aikata 3 da manual daya wanda hakan na iya haifar da rashin fahimtar aikin ga maaikatan zabe.
A bangaren talakawan gari mutane da dama suna ganin akwai wasu dalilai da zai sa suyi kokari wajen ganin sun kawo sauyin gwamnati musamman al-ummar Arewacin Nigeria, wanda suke ganin ma babu wani mai hankali da zai kara zabar jam’iya mai ci a yanzu domin ikirarin da suke gani a shekara 8 da wannan jam’iya tayi mulki basu amfanawa talakawa wani abun azo a gani ba sai koma baya, tsananin rayuwa da tashin kaya masarufi da dai sauransu. A duk kwanakin da suke shudewa a cikin wannan yanayi Jam’iya mai mulki tana kara samun koma baya a bangaren mutanen saboda tsananin wahalar da akesha a yanzu daya rage kwana 3 kacal babban zabe.
Ana gab da shiga wannan zabe ne akaji Dan Takarar PDP Atiku yana cika baki da bugun karji kan shifa yafi karfin Dan Takararsa na APC Bola Tinubu har yake ganin koda sau 100 zaayi zabe tskaninsa da Tinubu to tabbas shine zaiyi nasara, hakan yasa wasu mutanen suke mamakin wannan Magana tasa har suke cewa to kenan da Tinubu kadai yake ganin zai goga ina ya bar dan Takarar NNPP wato Kwankwaso da kuma dan takarar LP Peter Obi. Babban hasashen da jamaa sukeyi kuwa shine abinda Hausawa suke fada na Dan Hakkin daka raina na iya faruwa dashi Atikun domin Kwankwaso da Peter Obi ba ababan rainawa bane a wannan zabe domin kuwa suma sunada magoya baya kuma musamman Kwankwaso kullum suna Karin samun goyon baya daga talakawan gari dama wasu jiga-jigai a manyan jam’iyu.
Zaben Gwannoni Kuma ya rage sati 2 da kuma kwana 3 yayinda manyan yan takara suka cigaba da yakin neman zabe (Campaign)
Anan Kano babban abinda yake yawo a wajen mutane shine hukuncin da babbar kotun kasa ta yanke kan wanda zai tsayawa jam’iyar PDP takarar tsakanin Muhammad Abacha da Sadiq Wali inda kotu ta tabbatar da Sadiq Wali a matsayin halattaccen dan takarar gwamnan Jihar Kano wanda hakan yasa wasu jiga-jigan dake bayan Muhammad Abacha suka fice daga Jam’iyar zuwa sabuwar Jam’iyar NNPP domin a ganinsu uwar Jam’iya basuyi musu adalci ba kasancewar suna ganin kamar anyi amfani da karfin da tsagin Sadiq Wali suke dashi a jam’iyar wajen yi musu kamshin mutuwa, su kuwa hakan yasa suka fice suka bi tsohuwan mai gidansu Rabiu Kwankwaso, su kuma yan tsagin Aminu da sukayiwa nasara suke ganin yan tsagin Abacha sun cucesu wajen hargitsa musu jam’iya da bijiro da yan takarar bogi domin rabawa mutane hankali misali a karamar hukumar Tarauni , Adam Zaki ne dan takarar Majalissar jaha kwatsam kuma sai jiya muka wayi gari ana yawo da poster wani dan takarar daban shima karkashin jam’iyar ta PDP, tsagin Aminu Wali sun cigaba da cewa sun bata musu lokaci wajen rashin samun cikakkiyar damar yakin neman zabe (campaign) wanda suke ganin matukar suka fadi zabe to fa wannan dalilin ne yasa domin Jama’ar gari da dama har yanzu basu san waye halattaccen dan takara ba bare ma suyi tunanin kada masa kuri’a, domin a Kano maganar yan takara 3 kacal akeyi Abba, Gawuna da kuma Sha’aban.
Saidai masu hasashe fa suna ganin sauran yan takarar dake kananun jam’iya irinsu Mal. Ibrahim Khalil su Salihu Tanko Yakasai suna iya kawowa duk mai kokarin cin zabe cikas domin suma sunada nasu jama’ar a boye kuma har gobe dukkansu kowa yana sa rai da lashe wannan zabe. A bangaren Jam’iyar APC kuwa dan takara Gawuna yana iya kokarinsa wajen shiga kauyuka da tabbatar musu da kudirinsa na dorawa akan inda mai Girma Gwamna ya tsaya kuma yana musu alkawarin tallafi ga mata da matasa yayinda jamaa suke ganin wannan fa bakomai bane face yaudara domin suna ganin a mulkin yanzun ma basu amfana ba bare kuma wanda suke tunanin idan Gawuna ya koma mulki to fa zaaci gaba da shan wahala da kuma kamshin mutuwa ga mutanen musamman yan Adaidaita Sahu da kuma wanda ake tashin su daga wajen sana’arsu ba tare da an nema musu wani ba, kuma tabbas wannan na iya kawo cikas ga kudirin shi dan takara duba da yawan yan adaidaita Sahu a Kano state
A halin yanzu yan Adaidaita Sahu suna cewa babu mai hankalin da zai zabi wannan gwamnati.
Ta bangaren Sha’aban Sharada na ADC kuwa jama’a sun ce sun ji shiru wanda haka ya dawo dasu kan zargin da sukeyi tun a farko na cewa takararsa bata gaske bace inda suke gasgata kewa kamar kwangila aka bashi domin ya kawowa jam’iyar APC cikas a wannan zaben tunda yanzu sunji shi baya wani motsi a lokacin da suke ganin ya dace fa ace ya motsa duba da kwanaki kadan ya rage wannan zabe. Ta bangaren NNPP kuwa Abba Gida Gida kuma ya kara dagewa wajen shiga lungu da sako domin ganin ya kara jawo hankalin alumma domin su kara zabarsa a karo na biyu bayan daya samu ruwan kuri’u a zaben daya gabata, wanda hakan yasa mafi akasarin mutane suke ganin a wannan karon fa kowane dan takara saidai ya hakura ya barwa Abba dan suna ganin kamar yanzu shine lokacinsa, bugu da kari shigowar manyan jam’iyar PDP cikin tafiyar NNPP irinsu Sagagi da sauransu hakan ma yasa ya kara farin jini kuma mafi soyuwa a wajen alumma duba da yadda yake tara mutane a wajen taronsa.
Babban abinda yake kwantarwa da jama’a hankali shine kokarin da shugaban INEC yakeyi wajen ganin anyi zabe mai sahihanci a wannan kakar zaben kuma anyi yaki da amfani da yan daba da wasu yan siyasa sukeyi da kuma matsalar sace akwati da aringizon kuri’u domin hanyar daya daukko ta nuna amfani da naurar computer wajen tura sakamakon zabe zuwa ga INEC kai tsaye.
A wani bangaren Kuma hankalin Jama’ ya tashi sakamakon daukewar sadarwa wato network service da ake maganar zaayi daga nan zuwa Juma’a domin dai ganin anyi zabe mai sahihanci.
Wannan shine atakaice abinda ke faruwa a halin yanzu nan kasar dangane da wannan Zaben Mai zuwa.
March 1, 2023
Tun bayan kammala babban zaben shugaban kasa, sanatoci da kuma yan majalissar tarayya abubuwa da dama sun faru yayin zabe da kuma bayan zabe.
Daga cikin abubuwan da suka faru lokacin zabe sun hada da rashin kai kayan aikin zabe a lokacin zabe wanda ya saba da lokacin da akayi ka’ida na 8:30 inda wasu guraren sai 12 wasu 2 wasu ma 4 wanda hakan ya fusata masu kada kuri’a inda suke ganin yaya za’ayi su baro gidajensu tun 8 wasu ma basu karya ba amma ma’aikatan zabe da kayan zabe basu zo ba sai da lokaci ya kure , sannan kaidar kammala zabe shine karfe 2:30 sai dai duk wanda yake layi dole za’ayi masa amma sai da ta kai an kai har wajen karfe 9 na dare ana kada kuri’a, tabbas hakan ba karamin ci baya bane ga hukumar Inec saboda babu dalilin da zaisa su gaza shiryawa bayan lokutan da aka dauka wajen shirya wannan zabe, bugu da kari a kokarin da inec takeyi wajen ganin ta mayar da kowane akwati yawan mutane baifi 500 ba jama’a da dama an canja musu akwati yayinda aka kirkiri wasu sababbin akwatuna ba tare da mutane sun sani ba, mutane da dama sai sun je kada kur’ia za’ace musu wannan kuri’ar bata wannan akwati bace bayan sun yi shekara da shekaru suna zabe a wannan akwati, wasu an tura musu sako na canjin da aka samu wasu kuma an tura bai shigo ba wasu kuma basu iya samun damar karantawa ba, wannan dalilin yasa jama’a da dama ba suyi zabe ba musamman a Jihar Kano domin kuwa wasu daga inda tsohon akwatinsu yake zuwa inda sabon yake doguwar tafiya ce da tasa mutane da dama suka hakura da wannan zaben, sannan kuma a wannan zaben an samu karancin fitowa zabe fiye da zaben daya huce a baya hakan yanada alaka da mutanen suke ganin zabe a Nigeria bashida wani muhimmanci saboda dalilai guda 2, na daya (1) ta’addancin da wasu masu son zuciya suke sawa ayi a lokacin zabe inda jama’a suke ganin zama lafiya yafi zama dan sarki kara su zauna a gida basu fita ba bare aji musu ciwo a banza. Na (2) yawan magudin zaben da ake samu wasu ma suna cewa tun kafin zaben ma ansan wanda za’a bawa suke ganin babu bukatar su fita su bata lokacinsu kara a bawa duk wanda za’a bawa. A bangaren ma’aikatan zabe kuma an gaza biyansu hakkinsu na training da kuma allowance na cin abinci wanda da yawa sai ranar zabe da safe sannan aka basu wannan kudade wasu kuma har yau ma baa basu wannan kudade ba kuma da yawa sun yi doguwar tafiya sun kashe kudin mota daga gidajensu zuwa inda zasuyi wannan aiki, ga kuma kudinsu na zabe ma ba’a basu ba har kawo yau, gurare da yawa an samu tangardar naurar tantancewa (BVAS) yayinda wasu guraren kuma ba’a bada isassun kayan aiki ba kuma gurare da dama an samu matsala wajen basu littafin shigar da sakamakon zabe inda aka dinga bada wanda bana wannan akwati ba. Babbar matsalar da INEC ta gaza cikawa itace ta dora sakamakon zabe a internet immediately bayan gama zabe domin kuwa wasu masu amfani da BVAS din basu samu cikakken horo akan naurar da har zasu san yadda zasu dora wannan zabe wasu kuma inda suke babu network da zasuyi connecting su dora wannan sakamakon zaben, wannan matsalar tasa a wajen tattara zabe wakilin PDP Dino Malaye yake korafi akan meyasa baa dora sakamakon zabe a internet ba wanda yake ganin anyi hakan ne domin yin magudi a wannan zabe.
Babban abinda yaja hankali kuma ya bawa mutane matukar mamaki shine tasirin da kananan jam’iyu suka nuna a wannan zabe inda suka lashe zaben manyan jahohin da suke Nigeria guda 2 wato Kano da Lagos da kuma nasarorin da dan takarar Labour Party Peter Obi ya samu a manyan jahohin dake kasar nan ciki harda garin da ake ganin sunfi ko ina yawan jama’a a Nigeria Lagos, wannan nasarar ta bawa mutane mamaki kuma ya nuna kamar mutanenmu sun fara wayewa wajen ganin sun zabi chanchanta ba jam’iya ba. Sannan abun daya faru a jahohin kudu yasa masu hankali a cikin jama’ar arewacin Nigeria sun fuskanci inda aka dosa a yanzu, har akaji wani professor yana ikirarin abinda yan kudu sukayi hankali suka koyawa yan arewa domin su basa hana dan kasa yin register zabe wanda hakan ya basu dammar tara kuri’u mai yawa, inda professor din yake cewa tabbas wannnan abu daya faru yasa sun gane a zabe mai zuwa har almajirai sai sunyi musu register katin zabe kuma zasu jajirce wajen nunawa nasu soyayya domin kuwa soyayyar da inyamurai suka nunawa peter obi ce tasa ya samu nasara a guraruwa da dama ciki harda Arewacin Nigeria kamar Abuja, plateau da kuma Jahar Nasarawa. Idan mukayi duba da Jahar Kano wannan zabe ya bada mamaki matuka ganin yadda al’ummar jahar Kano suka karbi tafiyar sabuwar jam’iya wanda aka dade baaga hakan a shekaru da dama tun zamanin Abubakar Rimi. Sabuwar Jam’iyar ta lashe kusan kaso 90% na kujerun yan majalissa da suke jahar da kuma lashe Sanata 2 a cikin 3 dake jahar, zaben daya yamutsa hazo wanda har yanzu ake tattaunawa akansa shine zaben Tudun Wada da kuma Doguwa wanda ake zargin dan takarar majalissa wannan karamar hukuma yayi amfani da matasa wajen aikata ta’addanci a wajen wannan zabe domin ya samu nasara, abin ban haushi shaidun gani da ido sun tabbatar da an ganshi shi da kansa yana harbi a wajen wannan zabe kuma an tabbatar da akwai mutumin da aka harbeshi yana sallah a wannan waje bayan mutanen da aka kulle daki aka kunna musu wuta, wannan ba karamin ci baya bane a tsarin democracy kuma ya sava da dokokin kasa wajen amfani da ta’addanci a lokacin zabe da kuma ba lokacin zabe ba, al’ummar Nigeria dai sun zuba ido domin ganin hukuncin da zaa dauka akan wannan dan majalissa domin kuwa INEC ta tabbatar dashi a matsayin zababben wannan yanki, har yanzu dai ana bincike inda shi wannan dan takara yake tsare a hannun jami’an farin kaya (DSS).
A jiya daddare aka kammala karbar sakamakon zabe kuma aka tabbatar da wanda yayi nasara a wannan zabe amma fa akwai hujjoji da suke nuna yadda aka tafka magudi a wannan zabe inda akaji jam’iyar PDP da LP suna ikirarin lallai a soke wannan zabe a sake wani ko kuma su garzaya kotu. Kadan daga cikin sakamakon garuruwan da ake gani an tafka wannan magudi sun hada da Jahar Ekiti inda wakilin PDP Dino Malaye yace sakamakon da INEC ta wallafa a shafinta ba shine aka kawo gaban shugaban zabe ba, inda a gefe guda ma akaji tsohon shugaban kasar Nigeria Obasanjo ya soki wannan zabe kuma yayi umarni da lallai shugaban INEC ya soke wannan zabe gaba daya a sake wani domin bai yarda da ingancinsa ba yayinda su kuma jam’iya masu mulki sukayi masa martani da bashida darajar da zaisa a soke zabe, Kungiyar European Union (EU) ma tana cikin kungiyoyin da suka soki wannan zabe inda sukace akwai kuskure da dama da kuma rashin ingancin zaben duba da an samu satar akwati a gurare da dama kuma mutane sunyi korafi kala-kala akan zaben da dai sauransu.
Babban abinda mutane suke korafi akai shine zaben Jahar Gombe inda baturen zaben da kansa ya ayyana mutane 295,782 sune adadin wanda akayiwa register yayinda aka tantance mutane 78,487 amma bisa mamaki sai aka samu adadin valid vote 88,991 wanda aka samu Karin akalla mutane 10,000 da wani abun akan wanda aka tantance, to abin tambayar shine tayaya wannan mutane 10,000 din sukayi zabe ba’a tantancesu ba bayan a dokar wannan zabe matukar na’urar tantancewa BVAS bata tantance ka ba saidai kayi hakuri, kuma mutane suke mamakin yadda aka karanta wannan sakamakon a gaban shugaban shugaban INEC kuma ya karba ba tare da yayi korafi akan hakan ba, hakan ya bawa mutane gamsuwa akan video da suke yawo a kafefen sadarwa na an bawa yara kuri’a suna dangwalawa duk da ba’a tabbatar da wannan video daga wane gari ya fito ba, sai ma aka jiyo Jam’iyar APC suna bada umarnin a kama Dino Malaye da Dele Mammadu bisa zargin tada tarzoma a lokacin karbar zabe a Abuja. A safiyar yau kuma aka tashi da zanga-zanga a garin Abuja inda suke zargin Shugaba Buhari da kuma shugaban INEC bisa rashin cika alkawarin da suka dauka na gabatar da sahihin zabe, har suke ikirarin lallai shugaban INEC ya ajiye aikinsa.A karshe dai an kammala karbar zaben Jahohi 35 harda Abuja inda Dan takarar APC Bola Tinubu ya lashe wannan zabe da kuri’u 8,794,726. Sai Dan takarar PDP Atiku Abubakar ya samu kuri’u 6,984,520. Sai dan Takarar Labour Party Peter Obi ya samu kuri’u 6,101,533. Sai dan Takarar NNPC Rabiu Kwankwaso ya samu Kuri’u 1,496,687. Bola Tinubu ya lashe zabe a jahohi 12, Atiku Abubakar ya lashe jahohi 12, Peter Obi ya lashe Jahohi 11, Rabiu Kwankwaso ya lashe Jaha 1, yakama jahohi 36. Wasu daga cikin Mutanen Jami’iyar PDP suna zargin Rabiu Kwankwaso da hanasu lashe zabe wanda koda ace an hada kuri’un Rabiu Kwankwaso a bawa Atiku kuri’un bazasu kai na Bola Tinubu ba.
Like this:
Like Loading...